SiyasaAsiya
Gobara ta halaka mutane da dama a gidan wasan yara a Indiya
May 25, 2024Talla
Magajiyar Garin Nayana Pedhadiya, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa adadin mutanen ka iya zarta hakan, inda ta ce sun sha alwashin hukunta duk wanda ke da hannu a tashin gobarar.
Karin bayani: Indiya: Gobara ta kashe mutane 27
Wasu hotunan da aka wallafa a kafar talabijin ya nuna yadda hayaki ya turnuke sararin samaniyar gidan wasan yaran a yammacin wannan rana ta asabar, inda gobarar ke ci gaba da tashi cikin gaggawa.
Karin bayani: Indiya: Gobara ta kashe masu jinyar corona
Firaiminstan Indiya Narendra Modi, ya ce gwamnati na ci gada da daukar matakan kula da wadanda ke da sauran numfashi a yayin hadarin tare kuma da nuna alhini kan iyalan da suka rasa 'yan uwansu sakamakon tashin gobarar.