Gobara ta tashi a Koriya ta Kudu
January 26, 2018Talla
Masu aiko da rahotannin sun ce da dama daga cikin marasa lafiyar sun mutu a lokacin da ake kokarin cetonsu. Shugaban kasar na Koriya ta Kudu Moon Jae-In ya bayana takaicinsa a game da abin da ya faru kana kuma ya kira taron gaggawa na majalisar ministocinsa. Sai dai kuma kawo yanzu ba a san dalilan tashin wutar gobarar ba.