Gobe za´a shiga kwana na 4 a tattaunawar nukiliyar Koriya Ta Arewa
February 10, 2007Talla
An dage zaman taron kasashe 6 da nufin shawo kan kasar KTA ta yi watsi da shirin ta na nukiliya, har zuwa gobe lahadi, ba tare da an samu wani ci-gaba bisa wannan manufa ba. Rahotannin sun yi nuni da cewa KTA ta nuna niyar yin watsi da shirin ta na nukiliya don a saka mata da jerin taimako. To sai dai daya daga cikin abubuwan dake hana ruwa gudu shi ne game da takamaimen taimakon da za´a bawa gwamnatin Pyongyang idan ta kwance damara. Baya ga KTA da China mai masaukin baki, kasashen KTK da Amirka da Japan da kuma Rasha na halartar zauren tattaunawar a birnin Beijing.