1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban Najeriya Jonathan na tunanin sake yin takara

April 22, 2022

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce ya fara tuntuba da nufin sake tsayawa takara a zaben shugaban kasar na shekarar badi, abin da ke zaman alamun rikicin da ke tafe cikin fagen siyasar kasar.

https://p.dw.com/p/4AJeN
Goodluck Jonathan
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Wani gungu na matasa ne dai suka kai ga sammako a ofishi na Jonathan din da nufin neman tilasta masa sake tsayawa takara ta shugaban kasar a zaben 2023.

Daruruwa na matasan da ke dauke da hotuna na tsohon shugaban kasar dai sun ce sun tuna  bara ta zaki na tsohuwa ta gwamnatin Jonathan da tsada ta rayuwar da suke fuskanta yanzu, wajen sake jawo malafar bisa mulkin tarrayar Najeriyar.

"Suna na isa Abdulmutallib ni dan Katsina ne na zo taron Goodluck Jonathan ne saboda ina sonsa ya zama shugaba kasarmu. Muna kishinsa ne, mun ji dadin wa'adinsa na farko, kuma yanzu muna farin ciki, muna son ya sake dawowa ya zama shugaban kasa. Kuma za mu taya shi da addu'a."

"Suna na Umar Adams Izge daga Borno, na zo ne don in marawa tsohon shugabanmu baya domin har yanzu muna yinsa saboda mun yaba da mulkinsa."

To sai dai kuma in har ganyen da baya ya kai ga rubewa, ya sake tsira tare da yin kore shar  a tsakanin matasan da shugaban da 'yan kasar suka kora shekaru bakwai can baya.

Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele JonathanHoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Jonathan din dai yaki fitowa fili domin amsa kiran na abokan takun nasa.

"Eh, kuna kira na da in sake tsayawa zabe a shekarar badi, ba zan fada muku eh yanzun ba, kugen na siyasa ya fara bugawa, kuma ku ci gaba da sanya idanu. Amma dai rawar da za ku taka ita ce ta addu'a ta yadda Najeriya za ta samu mutumin da zai kula da harka ta matasa, mutumin kuma da zai yi aiki tukuru wajen warware matsaloli na mutane. Za mu yi aiki tare."

Ana dai kallon takarar ta Jonathan da hotunansa suka cika hedikwatar jam'iyyar APC mai mulki dai na iya raba kai walau a cikin APC ta masu tsintsiyar ko ita PDP da ya mulka tsawon shekaru guda shida.

Masu siyasar arewacin tarrayar Najeriyar dai na kallon mulki na shekaru hudu na Jonathan damar sake komawa mulki a kasar, a yayin kuma da 'yan uwansa dake kudu ke masa kallon mutumin da ke shirin bata ruwa a cikin burin kaiwa guda takwas a bangare na kudancin tarrayar Najeriyar.

To sai dai kuma a fadar Farouk BB Farouk da ke sharhi bisa siyasa ta kasar, takarar ta Jonathan na zaman mai hatsari har ga arewacin kasar da ke cikin matsala ta tsaro da tattali na arziki.

"Mutanen da suke ganin cewa su suke son yi wa Jonathan wannan alfarmar suna manta cewar duk a rayuwarsa ba wadanda suka yi masa kutingwilar rasa abin da ya fi so a rayuwarsa watau mulki irin mutanen Arewa maso yamma.

Taron ECOWAS Accra, Ghana Accra
Goodluck Jonathan ya zama wakilin ECOWAS a sansanta rikicin siyasar kasar MaliHoto: Nipah Dennis/AFP/Getty Images

Na san dai shugaban kasa dan wurin ne wadanda suke tunanin daukar wannan rashin basira a nan suke. A nan aka kada Jonatahn, a nan aka ci mutuncin siyasarsa, kuma ina tabbatar maka cewar in ka ba shi dama ya samu mulki to zai yi kokarin rama wannan abin.

Ya muka kare ma da Obasanjo wanda muka dauko daga kurkuku muka ba shi shugaban kasa amma kuma bai manta da abin da ya ce Abacha yai masa ba"

Tsohon shugaban dai na zaman na kan gaba cikin danyen ganye da jami'ai na gwamnatin da ke mulki yanzu da suka yi nasarar wanke shi daga aboki na adawa ya zuwa babban dan aike na takama cikin yankin yammacin Afirka.