GOYON BAYAN JAPAN WA AMURKA KANN KORIYA TA AREWA
November 25, 2003Bayan koriya ta arewa ta amince da mallakan makaman kare dangi tare da yarda dacewa tana rike da wasu yan kasar Japan cikin shekaru 20 da suka gabata,dangantaka na siyasa tsakanin Japan da Amurka na dada ingantuwa ,wanda ke karawa gwamnatin Bush na Amurkan goyon baya.A Zaa iya ganin hakan a taron da Washinton ta shirya a kasar Koriya,inda ministan harkokin jamaa Naoyuki Agawa tare da Directan yada labaru da Aladu dake ofishin jakadancin japan suka jadada bukatar sauyin mulki a kasar Koriya ta arewa,wanda injisu shine kadaiu zai kawo karshen rikicin na makaman kare dangi da kasar ke ikirarin mallaka.Agawa ya fadawa mahalarta wannan taro cewa dole ne a gaggauta sauyin mulki a koriyan.
Koda yake Agawa yana magana ne a madadain wakilin wannan cibiya ta Amurka da Japan,amma ba amadadin gwamnatin Japan ba,fitowansa fili karara yana neman a hambare gwamnatin shugaba Kim Jong na nuni da yadda halayyar ita Pyanyon ya fara shafan lamura na siyasar duniya.Yace japan ta fara karaya da harkoki koriya ta arewan ne bayan tayi gwajin makamanta masu linzami tare amincewa da cafke yan japan din a wannan kasa.Yace a karo na farko a shekaru 50 da suka gabata ,Japan ta razana,inda mutane da dama ke ganin cewa zaa iya sace yanuwansu daga wannan kasa.
A yanzu haka dai an kebe watan Disamba domin komawan kasashe 6 dake tattauna warware wannan riki da koriyan ke ciki.Tattaunawan zai hada da Amurka,Koriya ta kudu,Sin,Rasha,Japan da ita koriya ta arewan,dukkan kasashen dai na bukatar Pyanyong tayi watsi da makamanta na Nuclear,ayayinda ita kuwa take neman tabbaci na tsaro da tattalinta,idan har ana bukata tayi watsi da makamanta.
Wannan tataunawa dai a baya ya fuskanci matsaloli musamman adangane da rarrabuwan kai a gwamnatin Bush.Alokacin ziyararsa a yankin Asia shugaban na Amurka ya bayyana matsayinshi dangane da gwamnatin na Pyanyong.Yanzu dai ana jiran aga sakamakon zaman na kasashe shida,ko zai cimma tudun dafawa a rikicin makaman na Koriya ko kuma ya ruguje kamar na farkon irinsa daya gudana a Beijing.