Grace Mugabe ta fadi shari'a kan lu'u-lu'u
December 22, 2016Kotun kasar Zimbabuwe ta umurci matar shugaba kasa Robert Mugabe da ta maida ma wani dan kasuwa duk kadarorinsa da ta rike sakamkon rikici da ya hadasu kan wani zoben lu'u-lu'u wanda darajarsa ya kai miliyan guda da dubu 35 na Dollar. Ita dai Grace Mugabe ta ki karbar zoben da ta yi oda, tare da neman a biyata kudinta nan take.
Duk wani yunkuri da dan kasuwa Jamal Ahmed ya yi na biyanta kudinta daki-daki ya ci tura, lamarin da ya sa baya ga barazana daga jami'an tsaro, Grace mugabe ta kame wasu daga cikin benayen da ya mallaka: Sai dai kotu ta cematakin ya saba wa dokokin cinikayya.
Fadar shugaba Mugabe ba tace uffan ba tukuna dangane da wannan hukunci. Sai dai an saba ambato sunan Grace Mugabe a badakalar da ta shafi kayan kawa da kuma cin hanci da karbar rashawa. Sannan kuma an dade ana danganta Grace Mugbe da wacce zata iya maye gurbin maigidanta a takarar shugabancin Zimbabuwe. Ita ce ma yanzu haka take shugabantar reshen mata na jam'iyyar ZANU-PF da ke mulki.