Gudunmawar Amirka ga yaƙi da ta'addanci
June 4, 2013Yayin da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana goyon baya ga matakin gwamnatin Amurka na sa kuɗi dalar Amirka miliyan bakwai ga wanda ya taimaka aka kai ga kame jagoran ƙungiyar Boko Haram, masharhanta da talakawa na bayyana cewa matakin ba zai taimakawa ƙoƙarin kashe wutar rikicin ba.
Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ta bakin kakakin sa Rueben Abati ya goyi bayan matakin gwamnatin ƙasar Amurka na sanya zunzurutun kudi dalar Amirka miliyan Bakwai ga duk wanda ya bada bayanai da suka kai ga kame jagoran Kungiyar gwagwarmayan nan da aka fi sani da Boko Haram.
Shugaban ya haƙiƙance cewa matakin zai taimaka gaya wajen yaƙin da yanzu haka Tarayyar Najeriyar ke yi da ƙungiyar Jama'atu Ahlul Sunnan Lidda'awati Wal Jihad wanda aka fi sani da Boko Haram.
Yaya yankin Arewacin Najeriya ke kallon wannan mataki?
Sai dai wannan mataki bai samu goyon bayan yawancin al'ummar ƙasar ba musamman waɗanda ke yankin Arewacin kasar da suke ganin matakin a matsayin ingiza mai kantu ruwa da ƙasar ta Amurka ke yiwa Najeriya.
Yawancin al'umma kasar sun yi imanin cewa matakin na ƙasar Amurka zai ƙara hura wutar wannan rikici ne maimakon kawo karshen sa bisa la'akari da irin wannan matakan da kasar ta ɗauka a baya wanda kuma ba su taimakawa yaƙin da ake da ‘yan ta'addar ba.
Da dama na ɗaukar goyon bayan da gwanmatin Najeriya ta baiwa matakin ƙasar Amirkan a matsayin kasawa tare da yin sakaci a ƙoƙarin magance matsalar cikin gidan kasar. Malam Umar Adamu Shine shugaban ƙungiyar Malamin jami'an jihar Gombe.
Ra'ayin talakwan Najeriya dangane da wannan batu
Ga talakawan ƙasa kamar Malam Muhammad Mai kayan miyan Orji Quarters na ganin wannan matakin ba zai haifar da komai ba sai ƙara rura wutar rikicin.
A baya ma dai gwamnatin ƙasar Amurka ta sanya maƙudan kuɗaɗe kan wasu da take nema ruwa jallo sai dai hakar ba ta kai ga cimma ruwa ba. Wannan ya sa na tambaya malam Ibrahim Gombe kan irin tasirin ko akasin haka da wannan mataki zai yi a kokarin da ake da kawo karshen yaƙin da ake yi da Kungiyar Ahlul Sunna da aka fi sani da Boko Haram sai ya kada baki ya ce.
Na Kuma tambaya Malam Muhammad Bello Sarkin Arewan Bolari malami a sashin tarihi na jami'ar jihar Gombe ko kwalliya ta taba biyan kudin sabulu dangane da irin wannan mataki ? Sai ya ce.
A baya ma dai Tarayyar Najeriya ta ware kuɗi naira miliyan hamsin ga wanda ya bada bayanan da suka taimaka wajen kame Imam Abubakar shekau amma har yanzu shiru ka ke ji kamar an shuka dusa.
Mawallafi: Amin Mohammed Suleiman
Edita: Pinaɗo Abdu Waba