SiyasaAfirka
Guinea za ta karbi rigakafin Ebola daga Geneva
February 18, 2021Talla
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta sanar da haka a wannan Alhamis a wurin wani taro na musamman kan yadda za a tunkari sake bullar da Ebola ta yi a Guinea. WHO ta ce an yi nisa wurin kammala kawo rigakafin Ebolar 11,000 daga birnin Geneva na Switzerland a yayin da daga baya za a sake kai wa kasar ta Guinea allurai 8,000 da Amirka za ta sarrafa.
Wani jami'i a ma'aikatar lafiyar kasar Guinea Mohamed Lamine Yansane ya ce idan har sun sami rigakafin Ebola a ranar Lahadi to za su fara yi wa 'yan kasar a ranar Litinin mai zuwa ba tare da wani bata lokaci ba.
Wannan dai na zaman yunkuri ne na tunkarar Ebolar wace ta sake dawowa gida bayan ta yi wa kasar barna a shekarun 2013 zuwa 2016 lokacin da ta fantsama a kasashen Laberiya da kuma Saliyo.