Guinea ta fara kirga kwanakin ban kwana da Ebola
November 17, 2015Talla
Mahukuntan kasar Guinea Conakry sun tabbatar da cewa mara lafiya na karshe dauke da cutar Ebola ta samu sauki. Yarinyar 'yar shekaru biya da haihuwa da ke karkashin kulawa an sallame ta daga asibiti a wannan Talata, abin da ke nuna shiga matakin kirga kwanaki 42, bisa tsarin hukumar lafiya ta duniya, idan babu wanda ya sake kamuwa da cutar sai a fitar da kasar daga cikin wadda take karkashin annobar cutar ta Ebola.
Cutar Ebola ta yi sanadiyar hallaka fiye da mutane dubu-11 galibi a kasashen yankin yammacin Afirka, amma da taimakon kasashen duniya aka dakile cutar. A farkon wannan wata na Nuwamba kasar Saliyo ta samu nasarar ficewa daga cikin masu dauke da cutar, tun farko Laberiya ta samu irin wannan nasara.