Gurɓatar muhalli a Amirka
June 7, 2010Ɗanyen mai dake malala a gaɓar Tekun Mexiko yanzu haka yana barazana ga gaɓar Tekun jihar Texas ta Amirka. A karon farko tun bayan rugujewar dandamalin haƙan mai na kamfanin BP a ranar 20 ga watan Afrilu, yanzu haka an gano tsuntsaye jiƙe da mai a kusa da gaɓar Texas. Kawo yanzu jihohin Louisiana da Mississippi da Alabama da kuma Florida wannan bala'in ya shafa. Jami' ai a Amirka sun ce za a kwashe watanni kafin a shawo kan matsalar tsiyayar man da ke zama wani mummunan bala'i ga muhalli. Jami'in gwamnatin Amirka mai yaƙi da wannan bala'i Thad Allen ya yi gargaɗi da ka da a sanya dogon buri ga nasarar da kamfanin haƙan mai na BP ya ce yana samu wajen daƙile tsiyayar man.
Ya ce: "BP na samun ci-gaba amma ba za mu iya gamsuwa ba domin har yanzu mai na malala cikin ruwa. Man dai babban abokin gaba ne da ya mamaye kuma yayi garkuwa da gaɓar tekunmu."
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas