1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guterres: Gabas ta Tsakiya ka iya fadawa yaki

April 18, 2024

Sakataren MDD Antonio Guterres ya nuna damuwa kan halin da ake ciki a yankin Gabas ta tsakiya, inda ya yi gargadin rudanin da ake ciki ka iya rikidewa zuwa tashin hankali a yankin gaba daya.

https://p.dw.com/p/4ewc3
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres Hoto: Charly Triballeau/AFP/Getty Images

Gutteres ya ce luguden wuta da Isra'ila ke yi kan Falasdinawa a zirin Gaza a matsayin martanin harin da Hamas ta kaddamar a ranar 7 ga watan Oktoban 2023 ya jefa fararen hula cikin matsanancin hali musamman wadanda suka makale a yankin Falasdinu.

Gutteres ya kuma ce abun da ake bukata a bayyane ya ke, tsagaita wuta nan take a Gaza da kuma sako dukkan fursunonin yaki nan take tare da bada dama a kai kayan agaji.

Kasashen duniya suna da hakki da ya rataya a wuyansu na yin dukkan mai yiwuwa domin tabbatar da hakan.

Ya zuwa yanzu dai akalla mutane 33,970 aka kashe a yakin tsakanin Isra'ila da Hamas.