190412 Indien Raketentest
April 19, 2012Ita dai ƙasar ta Indiya ta jinkirta gwajin makamakin nata mai linzama da ta ƙera sakamakon rashin kyau yanayi. Amma kuma daga bisani ta cilla shi daga tsibirinta na wheller i zuwa tekun Indiya ba tare da wata tartibiyar matsala ba, kamar yadda Avinash Chander, shugaban cibiyar ASC da ta ƙera makamin da ke ɗauke a kan nukiliya ya bayyana.
"Wannan gwajin an yi shi cikin nasara. Mun gudanar da shi wannan na farko salin alin kamar yadda muka tanada."
Gwamnatin ta Indiya da ma al'umarta na alfahari da wannan ci gaban da ta samu, a ƙoƙarin da ta ke yi na kama kafar China a fannin makamaki mai linzami. Wannan ƙasa ta Asiya ta daɗe ta na ƙoƙarin shiga cikin ruƙunin ƙasashen duniya da suka ƙera makamin main inganci, wanda kuma zai iya cin dogon zango. A baya dai ta ƙera wasu guda biyu waɗanda nisansu ba zai fi na kilometa 3500 ba. Amma kuma makamain da ta yi gwajinsa a wannan alhamis, wanda ta laƙaba wa suna Agni na biyar, zai iya cin nisan kilometa 5000: ma'ana zai iya kai wa biranen shanghai da kuma Beijing na ƙasar China daga ƙasar ta Indiya. Ko shui ma Baghla Pallav, ƙwararre a fannin tsaron na Indiya, sai da ya zayyana yadda gwajin ya gudana dalla-dalla.
" Ko shakka babu, gwajin dai ya yi nasara. Wannan abin alfahari ne ga ƙasar Indiya da kuma masana kimiyarta. Da ƙarfe 08:07 aka cilla Agni na biyar daga tsibirin Wheller. minti 20 bayan haka kuma makamin ya faɗa cikin tekun Indiya."
Indiya ta tauna aya domin China ta ji tsoro
Tun dai bayan da Indiya ta fara tafiya kafaɗa da kafaɗa da obokiyar gabarta ta fil azam wato pakistan a fannin mallakar makamin ƙare dangi, aka san cewar babu makawa za ta nemi ƙera makamin da China ke alfahari da shi. Duk da cewa ƙasashen biyu wato Indiya da China na kishi tsakaninsu a fannoni da dama ciki kuwa har da na tsaro, amma kuma danganta ta inganta tsakaninsu a fannin tattalin arziki. sai dai har yanzu akwai tsumammiya tsakaninsu game da wani rikici na kan iyaka. Amma a haƙikanin gaskiya, yawan kuɗin da China ta ke kashe wajen saya da kuma ƙera makamai, sun ninka na takwarata ta Indiya. A cewar Raja Mohan, wani masanin siyasar Indiya, ƙasar na da niyar inganta makamin da ta ƙera domin ya yi daidai da na manyan ƙasashen duniya.
"Wannan baje kolin fasaha da muka gani yau, ya na nufin cewar Indiya za ta ci gaba da bunƙasa fusahar ta ta ƙera makamai masu cin dogon zango. Wannan tauna tsakuwa ne domin aya ta ji tsoro. A baya dai, Indiya ba ta da makamin da za ta iya afka wa China da shi."
Ya zuwa yanzu dai, ƙasashe biyar da ke da kujerar dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ne suka mallakai makaman ƙare dangi da kwe cin dogon zango, ciki kuwa har da Amirka, da Faransa, da Birtaniya, da china, da Rasha. Ana jin cewar Indiya na bukatar shekaru kafin makamin da ta yi gwaji ya kama kafafun na waɗanda ƙasashe biyar.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu