1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Indiya ta kafa dokar hana zirga-zirga a Kasmir

Zulaiha Abubakar MNA
March 5, 2018

Kasar Indiya ta kafa dokar hana zirga-zirga a wannan Litinin a yankin Kashmir sakamakon wata zanga-zangar adawa da gwamnati bayan sojojin kasar sun kashe wasu fararen hula a ranar Lahadi.

https://p.dw.com/p/2thGC
Indien Kashmir Protest
Hoto: Picture alliance/AP Photo/D. Yasin

Zanga-zangar ta samo asali tun bayan da daruruwan jama'a suka fantsama kan titinan kasar suna kiraye-kirayen kawo karshen mulkar yankin Kashmir da Indiya take cigaba da yi, lamarin da ya sanya jami'an tsaro suka fara harbi tare da jefa barkonon tsohuwa a kan fararen hula.

Shi dai yankin na Kashmir na rabe ne tsakanin kasashen Indiya da Pakistan, kuma wacce kasa na cigaba da ikirarin mallakar yankin gaba daya.

'Yan tawaye na cigaba yakar Indiya a kan yankin tun shekara ta 1989 tare da neman ganin an mallaka wa Pakistan yankin gaba daya, ko kuma ya zama yanki mai 'yancin cin gashin kansa, lamarin da sanya kasar Indiya zargin Pakistan da marawa 'yan tawayen baya.