Gwamnatin Iraki tana neman kawo karshen IS
February 19, 2017Talla
Firaminista Haider al-Abadi na Iraki ya bayyana cewa sojoji sun kaddamar da farmaki domin kwace yammacin birnin Mosul daga hannun tsagerun kungiyar IS. Hakan ya zo watanni hudu bayan sojojin sun farma birnin da ke zama tungar karshe na tsagerun na IS.
Kwace yammacin birnin Mosul zai zama wani aiki mai wahala saboda yadda masu ikirarin jihadi suka mamaye yankin, inda tuni aka kara yawan jami'an tsaro domin tabbatar da samun nasarar dakarun Iraki a wannan gagarumin aiki.