Kenya tana dauki mataki kan yaki da ayyukan ta'addanci
April 8, 2015Talla
Gwamnatin kasar Kenya ta rufe asusun ajiyan bankuna na mutanen da ake zargi da taimaka wa ayyukan ta'addanci, kwanaki bayan harin da ya hallaka mutane kusan 150 a jami'ar garin Garissa, abin da ake dangantawa da tsagerun kungiyar al-Shabaab masu kaifin kishin addin Islama. Akwai mutane 85 da kamfanoni wadanda aka rufe musu asusun ajiya, da kuma kimanin kamfanoni 13 masu hada-hadar aika kudade kasashen ketere.
Gwamnatin Shugaba Uhuru Kenyatta ta kuma dauki matakin kai hare-hare da jiragen saman yaki kan sansanonin 'yan al-Shabaab da ke cikin kasar Somaliya.
A jiya Talata daliban jami'ar kasar ta Kenya sun gudanar da maci domin tunawa da 'yan uwansu da aka hallaka tare da neman ganin an tsaurara matakan tsaro a makarantun kasar.