Pakistan ta shirya fara kidayar ‘yan kasar.
March 13, 2017Gwamnatin kasar Pakistan ta shirya tsaf don fara kidayar ‘yan kasar wacce ta yi wa lakabi da PAK-CENSUS.
Kidayar irinta ta farko a shekaru goma sha tara za a fara tane ranar laraba mai zuwa tare da taimakon rundunar sojoji data kunshi sama da soja dubu dari biyu don tsatstsauran matakin tsaro da shirin ko ta kwana.Kamar yadda kakakin rundunar sojan kasar manjo janar Asif Ghafoor da kuma ministar yada labarai suka bayyanawa manema labarai a wani gagarumin taron shirin kidayar cewar an raba shirin kidayar kashi biyu tare da ba da tabbacin kammala kidayar ranar 25 ga watan Mayu.
Da take Karin haske a kan yadda aikin zai kasance musammam ma a wannan yanayi na rashin yadda sakamakon hare haren da ‘yan ta’adda ke kaiwa bangarorin kasar,ministar yada labaran tace kowanne jami’in kidaya daya zai samu rakiyar soja a lokacin da za a dauki adadi da kuma bayanan iyalan kowanne gida.
Ta kuma yi gargadin cewa duk gidan da aka samu sun bayar da bayanan bogi ko sun boye wani abu to zasu fuskanci hukuncin zaman gidan kaso har na watanni shida.