Gwamnatin Syria ta yi alkawarin zaman lafiya
December 12, 2024Talla
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken wanda ya kai ziyara Jordan ya baiyana muhimmancin kauce wa duk wani abu da zai sake tada rikici a Syria.
Ya yi kalaman ne bayan sanar da cewa a baya bayan nan Israila da Turkiyya sun kai hari cikin Syria. Ya ce Amurka na son tabbatar da cewa ba a yi amfani da Syri a matsayin sansanin yan ta'adda da kuma tada hankalin kasashe makwabtanta ba.
A waje guda kuma Shugabannin kungiyar kasashen G7 masu karfin tattalin arziki na duniya sun ce a shirye suke su taimaka wa shirin da zai samar da gwamnati mai nagarta wadda za ta kunshi kowa da kowa a Syria ba tare da nuna bangaranci ko addini a sha'anin gudanarwar gwamnati ba.