Gyara ga dokar yaki da ta'addanci a Kenya
January 2, 2015Talla
Mai shari'a George Odunga ya ce kotun ta dau wannan matakin ne domin a ganinta bai kamata a ce an yi amfani da dokar wajen tauye hakkin dan Adam a kasar ba don haka ba za a yi amfani da sassan da aka jingine ba har sai alkalin alkalan kasar ya kafa kwamiti na mutum uku da za su duba ta don tantance sahihancin dokar baki daya.
Daga cikin irin abubuwan da alkalin ya jingine na dokar dai har da sashen nan da ya yi tanadin daurin shekaru uku ga manema labarai a gidan maza in sun watsa labarai da gwamnati ke ganin za su yi nakasu ga bincike da jami'an tsaro ke yi. Tuni dai 'yan jarida da kungiyoyin kare hakkin bani adama a ciki da wajen kasar suka yi na'am da wannan mataki da kotun ta dauka.