1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha da Kwango a kanun jaridun Jamus

Lateefa Mustapha Ja'afar MAB
November 11, 2022

Matsalar da ake fukanta wajen aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Tigray na Habasha ya dauki hankalin jaridun Jamus, baya ga rikici babu kakkautawa da ke wakana a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

https://p.dw.com/p/4JO52
Gwamnatin Habasha da 'yan fafutuka na TPLF sun cimma yarjejeniya a PretoriaHoto: SIPHIWE SIBEKO/REUTERS

Jaridar Die Welt da rubuta sharhi mai taken: Yarjejeniyar tsagaita wutar da babu ita: Ta ce yakin da ake yi a yankin Tigray na zaman guda mafi muni. A yanzu kungiyar Tarayyar Afirka na murnar cimma yarjejeniyar da za ta kawo karshen rikicin. Sai dai bangarorin da ke yakar juna ba sa cikinta. Jaridar ta ce: Kwanaki  biyu bayan cimma yarjejeniyar, wani likita daga yankin Tigray ya yi rubutu a shafinsa na Twitter cikin fushi, abin da ya disashe fatan kawo karshen yakin mafi muni da ake gwabzawa a Habasha.

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya da ke bayar da agajin gaggawa damin ceton rayuka, bai samu sahalewa daga gwamnatin Habasha da za ta ba shi damar shiga yankin Tigray ba. Likitan ya rubuta cewa: A kowanne minti muna rasa mara lafiya guda. Lokaci na kurewa a sashen bayar da agajin gaggawa da kuma bangaren wankin koda. Yarjejeniyar da bangaren gwamnatin Habasha da kuma wakilan kungiyar 'yan tawayen Tigray wato TPLF suka sanya wa hannu mai shafuka tara a birnin Pretoria na Afirka ta Kudu ta bukaci 'yan tawayen Tigray su ajiye makamansu su kuma aminci da shugabancin gwamnatin Habasha, kana su yi shirin kafa hukumar rikon kwarya.

Luftangriff trifft Mekelle, Region Tigray
Jama'a na duba wuraren da suka lalace bayan wani harin da aka kai ta sama a Mekelle,Hoto: Tigrai TV/REUTERS

Yankin Tigray ya sa mutane rasa matsugunansu

A nata sharhin kan rikicin na kasar Habasha jaridar die tageszeitung ta ce: Shekaru biyu na yaki, dubban mutane sun halaka. A yanzu 'yan tawayen Tigray na TPLF da firaministan Habasha Abiy Ahmed sun cimma yarjejeniyar sulhu. 'Yan tawayen Tigray su ajiye makamansu, sai kuma me? Yanayi a babban birnin yankin Tigray na tsakanin firgici da rashin yarda. Jaridar ta ci gaba da cewa: yaki na lalata wuri. Yaki mafi muni na yankin Tigray ya shafi dubban mutane. Da dama sun halaka, yayin da ya tilasta wa dubbai kaurace wa muhallansu. A tsawon shekaru biyu suna zama a wuraren wucin gadi da aka samar musu da kuma makarantu, inda suke samun tallafi daga Hukumar Raya Kasashe ta Amirka USAID.

Demokratische Republik Kongo | Proteste in Goma gegen UN Mission MONUSCO
Masu zanga-zangar na nuna rashin jin dadi da yadda ake wanzar da zaman lafiya a Goma.Hoto: MICHEL LUNANGA/AFP/Getty Images

Rikicin gabashin Kwango na kara ruruwa

Rubdugu a kan 'yan tawaye masu rike da makamai a yankin gabashin Kwango, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung. Ta ce tawagar dakaru daga kasashen yankin gabashin Afirka sun hadu waje guda. Yankin gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ya kasance cikin yaki babu kakkautawa. A yanzu kimanin sojojin makwabciyar kasa Kenya 1000 sun isa Goma babban birnin yankin da ya kwashe tsawon shekaru 30 cikin rikici.

Jaridar ta ce rikicin da ya samu jerin rundunonin wanzar da zaman lafiya, ciki har da Rundunar Wanzar da Zaman Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya mafi girma. Su ma sojojin Kenya sun isa Kwango-Kinshasa, a matsayin rundunar farko ta hadakar sojojin kasashen gabashin Afirka da suka kai dauki domin yakar 'yan tawayen. Kimanin kungiyoyin tawaye 100 ne ke cin karensu babu babbaka a yankin gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar ta Kwango. A hannu guda, sojojin gwamnati na yakar 'yan tawayen M23. A karshen watan Oktoban da ya gabata, 'yan tawayen sun samu damar kara kutsawa cikin birnin Bunagana da ke kan iyaka da Yuganda. Tsawon kilomita 35 ne ya raba 'yan tawayen na M23 da garin Goma da ke kan iyaka da Ruwanda.

Namibia Windhoek | Proteste gegen Genozid Abkommen mit Deutschland
'Yan Namibiya sun yi Zanga-zangar adawa da yarjejeniyar kisan kare dangi da JamusHoto: Sakeus Iikela/DW

Rashin fahimta tsakanin Namibiya da Jamus

Ba mu karkare da sharhin jaridar die tageszeitung mai taken: Cimma daidaito na sake fuskantar suka. Magadan 'yan kabilar Herero da Nama da aka yi wa kisan kiyashi sun sabunta sukansu, tare da bukatar a sake sabuwar tattaunawa. Ita ma gwamnatin Namibiya, na bukatar a sake tattaunawa. Sai dai gwamnatin Jamus ba ta da niyya. Jaridar ta ce: Yarjejeniya da aka cimma da Namibiya da ke jira a sanya mata hannu tsawon shekara daya da rabi na rawa. Gwamnatin Namibiya, na neman a sake tattaunawa kan yarjejeniyar da aka cimma, tana fuskantar matsin lamba saboda yarjejeniyar hadin gwiwar da aka wallafa a watan Mayun 2021 da Jamus ta dauki alhakin kisan 'yan kabilar Herero da Nama a karon farko tare da alkawarin biyan diyya Euro miliyan dubu daya da 100 cikin shekaru 30.