Kokarin fara aiki da yarjejeniyar sulhu a Habasha
December 1, 2022Talla
Karbar makaman daga 'yan tawayen dai, na zaman wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya da bangarorin biyu suka cimma a watan Nuwambar da ya gabata. Rikicin na Habasha da aka kwashe tsawon shekaru biyu ana fama da shi, ya yi sanadiyyar asarar dimbin rayuka da dukiyoyi tare da tilasta dubbai kauracewa gidajensu.
Yarjejeniyar zaman lafiyar ta kunshi raba 'yan tawayen Tigray da makamansu cikin kwanaki 30, sai dai a nasu bangaren sun nunar da cewa hakan ba zai yiwu ba har sai bangaren gwamnati ya janye sojojin makwabciyar kasa Iritiriya da na yankin Amhara da ke makwabtaka da Tigray din da suka zo domin taya bangaren gwamnatin yaki.