1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha ta zargin Amurka da kudundune

Mahmud Yaya Azare ZMA
March 2, 2020

Fatar da ake da ita na kawo karshen takaddama kan rabon ruwan kogin Nilu tsakanin kasashen Habasha da Masar da Sudan ta disashe, biyo bayan kauracewar Habasha taron rattaba hannu kan yarjejeniyar.

https://p.dw.com/p/3YlUW
DW-Reportage Nilkreuzfahrt
Hoto: DW/E. Kheny

Haka kwatsam dai kasar ta Habasha, wacca ta fusata da gayyatar gaggawar da Amurka tayi mata na zuwa don sanya hannu kan yarjejeniyar da ta ce an mata kudundune kanta,  ta nemi a kara ba ta lokacin yin karatun ta nutsu ga daftarin yarjejjeniyar da aka tsara rattaba hannu kanta ranar 29 ga watan Febrairun da ya gabata a birnin Washington .

Yarjejeniyar da Amurka da bankin duniya suka shiga tsakani don cimma tsakanin kasashen uku, wato Habasha da Masar da Sudan, bayan an share kwanaki ana tattaunawa da juna, kan yadda za a gudu tare a tsira tare wajen cin moriyar ruwan kogin Nilun ba tare da cuta ko cutarwa ba.

To sai dai kasar ta Habasha ba ta tsaya ga janyewa daga taron zaman  rattaba hannu kan daftarin yarjejeniyar kadai ba, ta ma hada da sanar da yin gaban kanta wajen fara cika katafariyar madatsan ruwan nata da akewa lakabi da "Madatsar Ruwan Qarni", lamarin da ya fusata Amurka wacca har ta gargadi Habashan da ta guji daukar wannan matakin.

Allam Ahmed na ma'aikatar ruwan kasar Habasha, yana ganin cewa kasarsa ta dauki wannan matakin ne don fargabar kar ayi mata sakiyar da ba ruwa:

BG Grand Renaissance Dam | Der äthiopische Premierminister Abiy Ahmed Ali mit dem ägyptischen Präsident Abdel-Fattah al-Sisi (2018)
Hoto: Imago Images/Xinhua

"Abun da akai gwamman shekaru ana takaddama kansa, zai yi wuya ace cikin 'yan kwanaki ko makwanni an gama warwareshi baki daya. Batun madatsar ruwan Qarni batu ne da ya shafi 'yan kasar Habasha ba Amurka ba. Framinista Ahmed Abe, wanda ya sami lambar yabo ta Nobel ta zaman lafiya, baya so ya yi asarar kujerarsa a zaben da ke tafe, kan wannan batun na madatsarar ruwan Qarni, wacca har yanzu wasu 'yan kasar Habasha basu gamsu da dalilan jnkirinta fara cikashi da ruwa da gwamnatinsa ke yi ba, wadanda suke zargin ya mika wuya ga matsin lambar Amurka, wacca a gaskiya bata chanchanci wannan shiga tsakanin ba."

Kasar Masar, wacca a shekarar 1821 ta mamaye Sudan kan rikicin rabon ruwan kogin Nilun, ta kuma gwabza yakin da bata yi nasara ba da kasar ta Habasha a shekarar 1875, ta yi barazanar sake shiga yaki da kowaye, don kare  kasanta na ruwan kogin Nilun da take dauka a matsayin kahon zuciyarta.

Äthiopien Addis Abeba | Diskussion Blue Nile & Renaissance-Damm | Flaggen
Hoto: DW/G. Tedla

To sai dai kamar yadda Asma Husainibabbar edita ta jaridar Al'ahram ke gani, gwabza yaki kan ruwan na Kogin Nilu, ko ma kai hari da jirage don wargazashi kamar yadda wasu 'yan Masar ke ta yin kiraye kirayen kasarsu tayi, ba shine mafita bag a wannnan batu mai matukar sarkakiya:

"Babu wani batun sake shiga sabuwar tattaunawa kan wannan batun da an gama dashi. Abun da nake zatan bangarorin zasu iya sake yi, shi ne daukar matakan kauchewa yin a fasa kowa ya rasa, ta hanyar sake kwaskwarima a sigar yarjejeniyar, yadda zata biya bukatun kowane bangare."