1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadaddiyar Daular Larabawa: Ta rufe sararrin samaniya

Binta Aliyu Zurmi
March 23, 2020

Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya sun kara tsaurara matakan tsaro a wani mataki na dakile yaduwar cutar numfashi da ta zame wa duniya karfen kafa.

https://p.dw.com/p/3Ztsb
Dubai Airshow 2019 | Airbus
Hoto: Getty Images/AFP/K. Sahib

Hukumomin na Dubai sun sanar da dakatar da saukar jiragen fasinja a fadin kasar har na tsawon makwanni biyu, Kamfanin jiragen sama mallakar kasar shi ma ya sanar da zai dakatar da aiki a ranar Larabar da ke tafe. A hannu guda kuwa, Saudiyya  ita ma ta sanar da kafa dokar ta baci har nan tsawon kwanaki 21 daga wannan rana ta Litinin. Wannan dokar hana fita za ta fara ne daga karfe 7 na maraice zuwa 6 na safe.