Hadarin jirgin sama a Brazil
July 18, 2007Talla
Wani jirgin saman fasinja na kasar Brazil dauke da akalla fasinjoji 176 ya zame daga kann titin saukar jiragen sama inda ya kama da wuta a birnin Sao Paolo.
Jirgin kirar airbus A320 ya zarce hanyarsa ne bayan saukarsa ya kuma ratsa ta kan babban titi makare da motoci kafin ya shige wani gidan mai inda ya kama da wuta nan take.
Rahotanni sunce akalla mutane 200 ne suka rasa rayukansu wadanda suka hada da fasinjojin dake cikin jirgin da
kuma wadanda suke kasa.
Jirgin mallakar kanfanin TAM ya taso ne daga Porto Alegro daga kudancin Brazil.
Har ya zuwa yanzu dai babu wanda ya san abinda ya haddasa wannan hadari kodayake ana ganin cewa mai yiwuwa rashin kyan yanayi ne ya haddasa shi.Wannan shine hadari mafi muni na jirgin sama a kasar ta Brazil.