SiyasaAfirka
Hadarin mota a Masar ya hallaka gomman mutane
October 5, 2024Talla
Hadarin wanda rahotanni suka ruwaito motar ta kwace daga hannu direba kafin daga bisani ta kuma fada a dayan hannu da motoci ke tafiya ya auku ne sakamakon gudu mara kima da direban ke yi.
Kasar masar kamar wasu kasashen Afrika na fama da yawaitar hadarin mota akai-akai wanda ake alakanta shi da rashin kyawun hanya da ma rashin kula daga bangaren dirobobin.
Shekara guda ke nan a watan Oktoban bara wasu motoci makare da fasinjoji suka yi taho mu gama a wata babbar hanya da ke Cairo lamarin da nan take ya hallaka mutane sama da 30.
Karin Bayani: Hadarin mota fitina ga rayuwar dan Adam