Halin da ake ciki a Japan bayan girgizar ƙasa
March 15, 2011A ƙasar japan har yanzu ana cikin dar dar dangane da rashin tabbacin yadda alamura za su kasance tun bayan girgizar kasa haɗe da ambaliyar tsunami da ta daidai ta ƙasar a juma'ar da ta gabata, zuwa yanzu dai kasashen duniya da dama na gargadin jama'arsu da su ƙauracewa ƙasar, a waje guda kuma dagwalon tashar nukiliyar dake malala yana ci gaba da haifar da ruɗani akan rashin sanin abin da ka iya faruwa anan gaba.
Rahotanni daga ƙasar ta Japan sun nuna cewa yawan mutanen da suka rasa rayukan su asakamakon wannan bala'i ya haura mutum dubu 10, har yanzu dai makatan ceto na ci gaba da ayyukan zakulo wadanda ake zatan gine ginen da suka rushe sun turmushe su, baya ga wadanda ambaliyar ruwan tsunami da ta biyo bayan girgizar kasar ta yi awon gaba da su.
Wakilin sashin Swahili na gidan rediyon Deutsche Welle Ali Attas, wanda yanzu haka yake zaune a kasar ta Japan ya bayyana yadda mutane ke ta yin hijira daga Tokyo babban birnin kasar,
"Yace yawancin abokan aikina da na sani sun kauracewa birnin Tokyo, dama sauran birane dake maƙobtaka da da inda bala'in ya faru. A yammacin nan nake samun labarin cewa suna tururuwa suna barin Japan gaba ɗaya, a gaskiya akwai fargaba"
Yaya tsaurin lamarin yakai
Rahotanni sun bayyana cewa turirin dake fita daga fasashshiyar tashar nukilya dake kusa da Fukushima, ya kai wani mizani da zai iya haddasa illa ga bila'Adama, wanda masana suka ce ya ninka yadda ya kamata fiye da sau tkwas, haka ne ma ya sa mahukuntan ƙasar suka dauki matakin kwashe mutanen da ke zaune a wuraren dake da da tazarar kasa da kilo mita 20 daga tashar.
Haka kuma an bayar da umarni ga dukkan mutanen da ke zaune a wuraren dake da nisan kilomita 30 daga tashar da su kasance acikin gida.
Yanzu haka dai hukumomin kasar sun fara amfani da gishiri mai kunshe da sinadarin (Iodized Pottasium) ga mutanen dake zaune a wuraren da iska ke iya kada turirin, wanda ka iya haddasa cutar kansa. Sama da mutane dubu 140 ne aka gargade su da su kasance acikin gida domin kaucewa wannan balai.
Shin hatsarin zai shafi Afirka?
Ƙasashen duniya da dama dai na cikin haɗarin tasirin wannan bala'in da ya faru a kasar Japan, misali yadda masana suka ce iska za ta iya kada turirin har zuwa wurare masu nisa, ciki har da nahiyar Afrika kamar yadda Dr Iddi Mkilaha babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar Tanzaniya ya bayyana..
"Yace dole ne mu damu kwarai, musamman mu da muke da masaniyar yadda turiri ke tafiya, iska ka iya kada shi ya yi doguwar tafiya har zuwa nahiyar Afrika, koda yake hakan abu ne mai wuya, babban abin yi shine mu kula da nau'in abincin da ake kawo wa Afirka daga Japan da sauran kasashen dake makobtaka da ita"
Darasi ga sauran ƙasashe
Tuni dai kasasen dake da makamashin nukilya suka fara daukar matakin gani wane, domin a yau ne shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi shelar rufe wasu tasoshin nukilyar kasar guda bakwai har sai an tabbatar da cewa babu wata matsala. Merkel tace daukar wannan mataki yana da muhimmaci matuka, kamata ya yi kasashen Turai da duniya baki daya su bi bayan Jamus wajen daukar wannan mataki
Zuwa yanzu dai wasu kamfanoni jiragen sama sun fara kauracewa sauka a kasar ta Japan, kamfanin jirgin saman KLM dana Air France sun kwashe ma'ikatansu daga Tokyo babban birnin kasar, domin kaucewa halin rashin tabbas da ake ciki.
A ƙasa kuna iya sauraron sautin rahotannin kan Japan.
Mawallafi: Nasiru Salisu Zango
Edita: Usman Shehu Usman