1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki gabannin zaben Kenya

Yusuf Bala Nayaya
September 25, 2017

Tun Bayan da kotu a kasar Kenya ta yi watsi da nasarar da ta ba wa Shugaba Uhuru Kenyatta damar ci gaba da darewa a karagar mulki saboda gano jama'a na ta tambayar irin halin ake ciki gabannin sabon zabe.

https://p.dw.com/p/2kf4C
Wahlen Kenia
Hoto: DW

Babbar kotu dai a kasar ta Kenya ta yi watsi da nasarar da Uhuru Kenyatta ya samu a zaben ranar takwas ga watan Agusta, matakin da ya mayar da shugaban Kenyatta da Raila Odinga madugun adawa mataki guda wato duk masu jira ranar zabe ta gaba don sanin makomarsu a kwatin kuri'a. Shugaba Kenyatta dai ya ce 'yan adawa da kotu sun yi baki guda wajen ganin sun hana ci gaban demokradiya da 'yan kasar Kenya suka dauki lokaci mai tsawo suna fafutika ta ganin ta girku. A yanzu dai an sanya ranar 26 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a sake zabe.

Masharhanta dai na ganin al'amura sun tsaya a Kenya, 'yan kwangila ba sa samun aiki ballantana ayi magana ta biyan kudi da sauransu. Haka kuma ita ma hukumar zaben kasar kallo ya koma kanta musamman kan kura-kuren da al'umma ke ganin ta aikata da suka kai ga rushe sakamakon zaben na Agusta. 

A ranar Juma'a dai da ta gabata 'yan adawar ta bakin daraktan masu gabatar da karar jama'a a Kenya Keriako Tobiko sun nemi cikin sa'oi 72 a gabatar da karar jami'an hukumar ta IEBC wadanda ake zargi da tafka magudi a lokacin zaben na ranar takwas ga watan Agusta.