Halin rayuwa a Iraq
December 31, 2003Talla
A halin da ake ciki dai a yau laraba a kasar ta iraq rahotanni na cewa an sami musayar wuta a yayin da dubban jammaa ke gudanar da wani maci a Birnin Kirkuk .A bisa wannan halin kuwa a kalla mutane biyu sun rasa ransu cikin wannan yamutsin na yau .Ana dai samun rashin jituwa a tsakanin kurdawa da larabawa a hannu guda kuma da turkawan dake zaune a cikin garin na Kirkuk .Batun tabbatar da mulkin dimokaradiyya shine batu na farko dake rarraba kawunannan shugabannin yankin baki daya .kamar dai yarda babban Jamiin yan sandan yankin ya tabbatar da cewa bayan barkeware wannan musayar wutar a kalla wasu da dama sun sami raunika inda tuni aka kaisu Asibitin yankin don neman magani .Wata majiya ta tabbatar da cewa an sami wannan musayar wutar ne a yayin da aka bude wuta a Hq jamiyyar kurdawa wanda nan take masu gadin Hq suka mayar da martani .To sai dai a daura da wannan halin ne dakarun hadaka bisa jagorancin Amurka suka yiwa yanmin kawanya baki dayansa .Larabawan yankihn dai na nuna adawa ne da kasancewar yankin karkashin kurdawa maimakon gwamnatin tsakiya daga Bagadaza .Yawancin masu gudanar da wannan boren dai na cewa basa bukatar kasancewar kirkuk a matsayin taraiya .Suna masu cewa dole ne Kirkuk ya zama a karkashin daular Iraq A yanzu dai kurdawa na bukatar ganin yankin na kirkuk ya kasance mai cin gashin kansa wanda tun a yakin Gulf yankin ke taka rawa batare da sanin gwamnatin tsakiya ba a can Bagadaza .Suna dai samun wannan kariya ne daga Amurka da kawayenta tun bayan kammala wannan yakin a shekara ta 1991.Har kawo yanzu dai tsugune bata kare ba a kasar ta iraq tun bayan cafke sadam hussain tsohon shugaban kasar ta iraq .To sai dai wata majiya tace a yanzu dai komai ya farawa lafawa a kasar koda dai ana fuskantar yan tsirarun yan tawaye wadanda ake ganin cewa daga kasashen ketare suka malala cikin kasar .A wani labarin kuma a yau Laraba Pm kasar Thailand yace ba zai aike da dakarun kasar ba a cikin Iraq domin shiga fagen fama .Sai dai yace a yanzu haka akwai dakarun kasar wadanda ke bayar da tallafi na agajin gaggawa ga wadanda suka sami raunika a cikin yamutsin .Idan dai baa mantaba a makon daya gabata yan kasar biyu ne suka mutu bayan da motar dake dauke dasu ta taka wani Bom inda ya tarwatsa motar baki daya .
Talla