1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ta saki wasu Amurkawa da ta tsare

October 21, 2023

Kungiyar Hamas ta sanar da cewa ta saki wasu Amurkawa biyu da ta ke tsare da su. Kungiyar ta tsare su ne tun a ranar 7 ga watan Oktober bayan da ta kai hare-hare kan Isra'ila.

https://p.dw.com/p/4XqCJ
Judith da kuma Natalie Raanan da kungiyar Hamas ta saki bayan tsare su na wani lokaci
Judith da kuma Natalie RaananHoto: US Embassy in Jerusalem/AFP

Offishin firanministan Isra'ila ne ya tabbatar da sakin Judith da kuma Natalie Raanan. Tuni dai Shugaba Joe Biden na Amirka ya nuna fari cikinsa kan samun 'yancin mutanen. Alkalumman gwamnatin Isra'ila sun yi nuni da cewa, kimanin mutane 200 ne kungiyar ta Hamas ke tsare da su a zirin Gaza.

Karin bayani: Kasashe na tir da sabon rikicin Isra'ila da Hamas

A share guda, ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Bearbock na ziyara a Isra'ila domin nuna goyon baya ga gwamnatin kasar. Ministar na kuma ziyarar ce da nufin taimakawa Falasdinawa su samu damar samun kayan agaji.