Hamas ta za ta tura tawaga Masar domin ci gaba da tattaunawa
April 6, 2024Hamas wacce a baya ta kara jaddada matsayarta a kan bukatar tsagaita wuta na din-din-din da kuma janye dakarun Isra'ila daga Gaza da ma musayar fursunoni da 'yan Isra'ila da Hamas ke ci gaba da garkuwa da su, sharuddan da Isra'ila ta yi watsi da su.
Ko a jiya Juma'a shugaban Amurka Joe Biden ya aike da wasika ga jami'an diplomasiyyar kasashen Masar da Qatar da ke shiga tsakani a tataunawar da ake yi da su shawo kan Hamas don ta amince da wasu sharuddan Isra'ila domin kawo karshen wannan yakin da ke cika watannin na 7.
A daya hannun kuwa, ma'aikatar lafiya ta Hamas ta sanar da cewar ya zuwa yanzu Falasdinawa da suka rasa rayukansu tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da harin ramuwar gayya sun haura mutum dubu 33,000. tare da jikkata wasu sama da dubu 75,000.