1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta hana dan Osama izinin zama

Abdul-raheem Hassan
March 2, 2019

Tun watan Nuwamban shekarar 2018 Saudiyya ta soke yaron Osama bin Laden Hamza shedar izinin zama a kasar, amma matakin bai fito fili ba sai bayan da ya zama wanda duniya ke nema ruwa a jallo.

https://p.dw.com/p/3ELsa
Hamza bin Laden Sohn von Osama Bin Laden
Hoto: picture-alliance

Hamza na cigaba da yin tasiri cikin kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya, inda a baya-bayannan ya wallafa wani faifan murya da bidiyo tare da yi wa Amirka da sauran kasashen yamma barazanar fuskantar hari daga mabiyansa a matsayin daukar fansa na kashe mahaifinsa Osama bin Laden da ya jagoranci kungiyar al-Qaida. Sai dai haryanzu babu wanda ya san hakikanin inda Hamza ya ke boye.

Majalisar Dinkin Duniya ta shigar da sunan Hamza bin Laden cikin jerin sunayen mutanen da aka sa wa takunkumi bisa zargin ta'addanci, ita ma gamnatin Amirka ta yi shelar ba da kyautar dala miliyan daya a matsayin lada ga duk wanda ya kwarmata bayanan da zai taimaka a kama Hamza bin Laden.