APC tana neman kawo karshen rikicin da jam'iyyar ke fuskanta
November 3, 2021Da yawa cikin ‘yayan jamiyyar ta APC mai mulki sun dugunzuma tare da fusata, fushin da ya sanya mika ragamar jamiyyar a hannun kwamitin riko a jam'iyyar karkashin gwamnan jihar Yobe Mai Malla Buni domin gyara lamura, dama kafa kwamitin sulhunta 'yan jam'iyyar ta APC mai mulki a Najeriya. Irin yadda rigingimun suka sake daukan sabon salo a jihohi da dama da aka samu bangarori biyu ya nuna halin na rikicin jamiyyar. Alhaji Ahmadu Haruna Zago na cikin wadanda suka fusata a jam'iyyar ta APC duk da matakin da jam'iyyar ya dauka.
Karin Bayani: Najeriya: Zaben shugabannin manyan jam'iyyun siyasa a jihohi ya bar baya da kura
Tun bayan awon gaba da tsohon shugaban jam'iyyar Adams Oshimohole har yanzu da sauaran ‘yan jam'iyyar da ke jan daga a kan korafin da suke da shi, domin duk da mataki na haramta kai lamarin gaban kotu sun tirje sun ma ki janyewa. Sanata Abdullahi Adamu shine shugaban kwamitin sulhunta ‘yayan jamiyyar da suka gudanar da taro a kan aikin da ke gabansu a Abuja.
Rikici ko takadama akan ce gishiri ne ga dimukurdiyya musamman a tsari na cikin gida iri na jam''iyyu, da akan samu ra'ayoyi mabambanta.
A yanzu dai jam'iyyar APC na hali na kalon ganin iyakar gudunka da babbar jamiyyar adawa ta PDP ke ,mata wacce ta kammala babban taron na kasa tare da zaben sabbin shugabani a yanayi na cimma sulhu ga mafi yawan mukaman da aka zaba.