Hare hare a Agadez da Arlit na Nijar
May 23, 2013Wasu mutane da ake zaton cewar masu kaifin kishin addini ne da aka kora daga Mali sun kai hare-hare a wani barikin sojojin na garin Agadez da kuma a cibiyar kamfanin hakar uranium na SOMAIR da ke a garin Arlit. Rahotannin da muka samu sun nunar da cewar maharan sun tarwatsa wata mota a kofar barikin sojen na AGgadez kafin su kutsa ciki. An ta musayar wata tsakanin maharan da kuma sojojin Jamhuriyar ta Nijar. Yayin da a garin Arlit maharan suka tarwatsa wat mota a kofar kamfanin na SOMAIR.
Da misalin karfe biyar na safiyar wannan alhamis ne aka soma jin karar fashewar wasu
abubuwa da kuma harbe harban bindigogi a garin na Agadez. Sai dai kuma bayanan da wakilin DW ya samu sun nunar da cewar kura ta dan lafa bayan da sojojin gwamnati suka fatattki maharan.
Mawallafi:Gazali Abdou/ Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu