Isra'ila ta halaka fararen hula a birnin Jenin
May 22, 2024Hukumomi a yankin Falasdinu sun ba da rahoton mutuwar mutane akalla takwas a yayin hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai birnin Jenin da ke yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan da nufin farautar mayakan Hamas da kuma 'yan jihadin Musulunci.
A cikin daren Talata wayewar Laraba kungiyar agaji ta Red Crescent ta ba da rahoton cewa sojojin Isra'ila sun kai guda daga cikin hare-haren kan wata motar daukan marasa lafiya a lokacin da take korarin zuwa dauko wani da ya jikkata.
Karin bayani: Kotun ICC ta bada sammacin kama Netenyahu da jagororin Hamas
Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ce a maraicen ranar Talata an yi dauki ba dadi mai zafi tsakanin sojojin Isra'ila da mayaka da ke yanki sannan kuma an hango garimaren hayaki a sansanin 'yan gudun hijirar da ke birnin.
Kazalika kamfani yada labarai mallakin hukumomin Falasdinu na Wafa ya ruwaito cewa samamen na Isra'ila sun sa an rufe shaguna da makarantu da kuma sansanin 'yan gudun hijira na birnin na Jenin da ke yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan.