1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An halaka sojojin Nijar a Diffa

Salissou Boukari LMJ
May 20, 2020

Tun daga farkon azumin watan nan na Ramadana yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar ke fuskantar kai hare-hare daga 'yan ta'adda na kungiyar Boko Haram, inda cikin wannan wata kadai na Mayu suka kai hare-hare har sau uku.

https://p.dw.com/p/3cWrP
Niger Armee | Opfer nach Angriff
Wani harin 'yan ta'adda ya halaka sojojin Nijar a yankin diffaHoto: DW/S. Boukari

Yawaitar kai hare-haren da ake alakantawa da kungiyar Boko Haram kan sojojin Nijar, na ci gaba da janyo cece-kuce a tsakanin al'ummar kasar da ke ganin ya kyautu a dau mataki domin kawo karshen wannan matsala. Hari na baya-bayan nan dai shi ne na farkon wannan makon, inda da wajejen karfe 11 da rabi na dare 'yan ta'addan dauke da manyan bindigogi, suka kai hari kan sojojin da ke wani sansani sa ido na garin Bilabirim mai nisan kiminin kilomita 36 da Arewa maso Gabashin N’guigmi cikin jihar ta Diffa. Yayin wannan harin dai, sun hallaka sojojin na Nijar 12 tare da raunata wasu guda 10 kaman yadda sanarwar ofisin ministan tsaron kasar ta Nijar ta nunar, inda ta ce maharan sun kona kayayyaki da dama tare da yin awon gaba da wasu.

Sojojin da suka bace sun dawo

Sai dai bayan afkuwar lamarin sojojin da ke da cibiya a garin N'Guigmi, sun kai dauki tare da bin sawu, inda suka samu nasarar murkushe 'yan ta'addan bakwai, tare da kwato wata motar soja mai dauke da babbar bindiga. Sojojin na Nijar dai sun ci gaba da biyar sawun maharan domin murkushesu gaba daya da kuma karbo dukkannin kayayyakin da ke hannunsu, a cewar sanarwar ta gwamnati. Sanarawar ta kuma ce sauran sojojin da ake zaton sun bace ne, duk sun samu komawa sansaninsu lafiya.

Symbolbilder Niger Armee
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Sai dai da yake magana kan batun hare-haren da ake kai wa sojojin na Nijar, Kanal Habou Oumarou mai ritaya, wanda a yanzu ya kafa sabuwar jam'iyya mai suna PRDD don samun zaman lafiya da bunkasar kasa, ya yi kira da a sauya dabaru. A farkon wannan wata na Mayu ne dai wani harin na 'yan Boko Haram kusa da birnin Diffa, ya haddasa mutuwar sojojin na Nijar biyu cikinsu har da mai mukamin Laftanar, inda 'yan ta'addan suka kwashi kayayyaki masu tarin yawa na sojojin, kafin daga bisani su sake dawowa kwanaki kalilan bayan wannan hari.

Komawa Diffa ka iya zama mafita

Wannan Lamari dai, ya sanya ministan tsaro da babban hafsan hafsoshin na Nijar Janar Salifou Modi sun tare a Diffa domin sanya idanu tare da kaddamar da tsarin fatattakar 'yan ta'addan. A ranar 11 ga watan nan na Mayun dai, sojojin na Nijar sun halaka 'yan ta'addan da dama tare da kwace dimbin makama. Koda a karshen watan Octobar bara ma dai, 'yan ta'addan sun kai hari a sansanin sojojin na Bilabrin, inda a wancan lokacin ma sojojin na Nijar 12 suka kwanta dama, yayin da wasu takwas suka samu raunuka. Sai dai ana ganin matakin da babban jagoran sojojin na Nijar ya dauka zai taimaka gaya wajen gyara duk wasu kuraran da aka samu a yakin da ake da masu tayar da kayar baya a yankin Tafkin Chadi.