Hare haren bama-bamai a majami'un Kenya
July 1, 2012Wasu tagwayen hare haren bama-bamai da aka kaddamar a majami'u biyu na wani gari da ke arewacin Kenya sun haddasa asarar rayukan mutane 16 tare da jikata wasu da dama. Bisa ga bayanan da rundunar 'yan sandan kasar ta bayar dai, wasu 'yan bindiga da suke rufe fiskokinsu ne suka harba bama-bama a cocuna biyun na garin Garissa tare da bude wuta akan kiristoci da ke ibada a cikinsu.
Wadannan dai su ne hare hare mafi muni da Kenya ta fiskanta tun bayan da sojojinta suka fara sa in sa da kungiyar al-shabab a karshen shekara ta 2011. Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin wadannan hare haren. Sai dai gwamnatin Kenya na alakantasu da al-shabab ta Somaliya da ke ta tsattsauran ra'ayin islama.
kungiyar musulmin kenya ta yi tir da wannan danyen aiki da ke neman zaman ruwan dare a kasar.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman