1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren Dakarun Kenya ya kashe fararen hula

November 1, 2011

Gwamnatin Kenya zata binciki asarar rayuka sakamakon hare-haren sojojinta a yanikin kudancin Somaliya

https://p.dw.com/p/133KE
Raila OdingaHoto: AP

Priministan Kenya yayi alkawarin cewar, gwamnati zata gudanar da bincike dan gane da yiwuwar asarar rayukan fararen hula sakamakon kutsen da sojojin Kenyan suka yi a  Somaliya.

Kungiyar bada agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta sanar da komawa domin ci gaba da da raba abinci wa sama da mutane dubu 6 dake sansanin 'yan gudun hijira a yankin kudancin Somaliya, bayan janyewa da tayi sakamakon hare-haren ranar lahadi. A jiya ne dai kungiyar bada agaji ta likitoci ta Doctors without Boaders ta sanar da cewar, mutane 5 ne suka rasa rayukansu, ayayinda wasu 50 suka samu raunuka daga hare-haren da dakarun kenyan suka kai da jiragen yaƙi.

Sai dai priministan Kenya Raila Odinga da yayi nadamar kowace irin asara za'a iya fuskanta daga wannan kutse na kakkabe 'yan al-shabab daga yankin.

" Bayan kammala wannan aikin, Kenya bata muradin sojojinta su kara koda yini guda ne a Somaliya. Sai dai muna neman goyon bayan ƙasashen Duniya a fafutukar tamu ta kakkabe 'yan kungiyar tsageru na Al-shabaab daga wannan yankin. Kuma muna nadamar rayuka da dukiyoyi da za'a iya yin asara a yayin wannan faɗa".

Gwamnatin Kenyan dai tayi amanar kai somame da jiragen yaki ta sararin samaniyan kudancin Somaliyan a ranar lahadi, sai dai ta danganta asarar rayuka da akayi da mayakan kungiyar ta al-Shabaab.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita          : Usman Shehu Usman