Hargitsi a zauren majalisar dokokin Kenya
December 18, 2014Wakilan majalisar dokokin kasar Kenya sun ba wa hamata iska abin da ya sa aka dakatar da mahawara game da yi wa dokokin tsaron kasar kwaskwarima.'Yan adawa a majalisar sun yi ta jifa da takardu a zauren majalisar yayin da wakilan bangaren gwamnati suka naushe Saneta Johnson Muthama na 'yan adawa kana suka kece masa riga.
Shabir Shakeel wakilin 'yan adawa ne a majalisar dokokin ta Kenya yace "sun yi bakin ciki da abin da ya farun. An ci zarafin shugabanni da sanetocin 'yan adawa a zauren majalisa. Na yi matukar bakin ciki da abin da ya faru."
Gwamnati ta ce tsaurara dokokin tsaro zai taimaka wajen yaki da ta'addanci amma masu sukar lamiri na ganin matakin a matsayin wani yunkuri na rufe bakin masu rajin kare hakkin jama'a.
Gwamnatocin wasu kasashen yamma ciki har da Amirka da Birtaniya sun yi kira ga 'yan majalisar dokokin Kenya su mutunta hakkin dan Adam idan suka zo yi wa dokokin gyaran fuska.