1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a Libiya ya hallaka mutane da dama

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 2, 2018

Kimanin mutane 11 ne aka tabbatar sun rasa rayukansu sakamakon wani hari da aka kai a ofishin hukumar zaben Libiya da ke Tripoli babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/2x47q
Libyen zerstörtes Gebäude in Tripoli
Harin ta'addanci a birnin Tripoli na LibiyaHoto: Imago

Wata sanarwa da ma'aikatar lafiya ta Libiyan ta fitar, ta nunar da cewa baya ga wadanda suka mutu, mutane bakwai kuma sun samu munanan raunuka. Daga cikin mutane 11 da suka hallaka dai har da maharan da suka kai harin na kunar bakin wake su biyu, kamar yadda wani jami'in hukumar zaben ya shaidar. An ga hayaki ya turnuke sararin samaniya na ofishin hukumar zaben, cikin hotunan da gidajen talabijin suka nuna. Sai dai kawo yanzu babu masaniya kan wanda ya kai harin, koda yake dama kasar ta Libiya ta saba fuskantar irin wadannan hare-hare daga kungiyar 'yan ta'adda masu kaifin kishin addini.