1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a sansanin sojin Indiya

Ahmed SalisuJanuary 2, 2016

Wasu mutane dauke da manyan makamai sun afakawa sansanin sojin Indiya da ke kan iyakar kasar da makociyarta Pakistan.

https://p.dw.com/p/1HX32
Indien Luftwaffe Archiv
Hoto: Getty Images/AFP/Raveendran

Jami'an tsaro suka ce suna zargin maharan 'yan wata kungiya ce ta masu kaifin kishin addini da ke da cibiyarta a Pakistan kuma sun batar da sawu ne bayan da suka sanya kayan soji Indiya, lamarin da ya basu saukin shiga cikin sansanin sojin.

Masu aiko da rahotanni suka ce yayin ba ta kashin da suka yi da dakarun na Indiya dai, an samu asarar rai daga bangaren maharan da kuma jami'an tsaron Indiya kana sojin na Indiya akalla biyar sun jikkata kuma yanzun haka ana cigaba da bincike a wajen don ganin ko akwai karin wasu maharan da ke makale a cikin sansanin.

Wannan harin dai na zuwa ne mako guda bayan da firaminsitan Indiya Nerandra Modi ya ziyarci takwaransa na Pakistan din Nawaz Sharif, ziyarar da ake kallo a matsayin ta kyautata danganta tsakanin makotan biyu wanda suka jima suna kai ruwa rana.