Hari bam a birnin Bamako na Mali
April 3, 2015Talla
Wani bam da ya tashi ya yi sanadiyar hallaka mutane biyu a birnin Bamako fadar gwamnatin kasar Mali.
Wani jami'an soji ya ce wani mutum da yake dauke da ababen fashewar tare da wata mata suka hallaka. Tuni sojojin kasar da na Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin tabbatar da zaman lafiya suka kawanya wa gidan.
Kasar ta Mali da ke yankin yammacin Afirka tana fuskantar tashe-tashen hankula daga kungiyoyin tsageru da ake dangantawa da kaifin kishin addinin Islama.