1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari na biyu a yini guda a Nairobin Kenya

October 24, 2011

Kamar a harin da aka kai da safiyar litinin a Nairobi, na yamman wannan rana ma ya jikata mutane kalilan a babban birnin na Kenya. Hukumomin wannnan kasa sun zargin kungiyar al-Shabab da kai wadannan tagwayen hare-hare.

https://p.dw.com/p/12y5a
Kenya ta sha alwashin mayar da martani ga al-Shabab na somaliyaHoto: dapd

Wani gurneti ya sake tashi a tsakiyar birnin Nairobi na Kenya sa'o'i kalilan bayan wanda ya jikata mutane 12 a wani gidan shakatawa da ke tsakiyar birnin. Kafofin watsa labaran Kenya sun nunar da cewa gurneti ya tarwtase ne a wani wurin jiran bas, yayin da na safe kuma, wani mutun da ba a tantance ko wane ne ba, ya jefa shi tare da ranta ana kare.

Wadannan tagwayen hare-haren su zo ne dai kwanaki biyu bayan da ofishin jakadancin Amirka a Nairobi ya yi gargadin afkuwan hari a babban birnn na Kenyai. Dama dai kungiyar al-shabab ta yi barazanar kai wa kenya hare-hare idan ba ta dakatar da haren da ta ke kadmmarwa a Somaliya ba.

Hukumomi a Nairobi suna dora alhakin harin a kan kungiyar  Al-Shababa wacce ake zargi da satan baki daga kasar Kenya, tare da barazanar yin kafar ungulu ga arzikin da kasar ta ke samu daga sashinta na  kula da shakatawa da yawon bude idanu.

Dakarun Kenya sun kori 'yayan kungiyar ta Alshabab zuwa Somaliya, kuma kungiyar ta yi barazanar kai hare-hare idan har dakarun na Kenya basu daina fatattakarsu ba. Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin wannan hari

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Yahouza Sadissou