Ta'addanci
'Yan ta'adda sun kashe mutane 15
May 22, 2023Talla
Kimanin mutane 15 suka halaka galibi makiyaya a yankin gabashin kasra Burkina Faso kamar yadda majiyoyin tsaron kasar suka tabbatar.
A irin wannan hare-haren na 'yan ta'adda aka halaka kimanin mutane 20 ranar Jumma'a ta makon jiya a yankin gabashin kasar. Ita dai kasar ta Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka tana fama da matsalolin tsaro sakamakon hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi.