SiyasaAfirka
Mutane sun halaka a Burkina Faso
September 21, 2023Talla
Gwamnatin ta Ouagadougou ta kuma yi ikirarin kashe 'yan ta'adda goma sha biyu, a wani martani da sojojinta suka mayar ga 'yan ta'addar bayan hare-haren biyu. Masu ikirarin Jihadi dai sun addabi Burkina Fasoda munanan hare-haren ta'addanci, inda ya zuwa yanzu suka yi sanadin mutuwar fararen hula da sojoji sama da 17,000 a cikin shekaru takwas da suka gabata.
Hukumomi na ci gaba da karfafa matakan samar da tsaro kananan hukumomin da ‘yan gudun hijirar suka koma matsugunansu domin kare rayukansu da dukiyoyinsu.