1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 14 sun mutu a harin Boko Haram

October 13, 2020

Manoma goma sha hudu ne harin Boko Haram ya hallaka tare da yin garkuwa da wasu goma sha biyar wasu da dama kuma na kwance a asibitin garin Ngwom kusa da Maiduguri inda lamarin ya faru.

https://p.dw.com/p/3jqjH
Nigeria Islmischer Staat in West Afrika ISWAP Truck
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Wani sabon hari da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram da kaiwa ya hallaka wasu manoma goma sha hudu a kauyen Ngwom da ke da tazarar kilomita sha hudu daga Maiduguri babban birnin jihar Borno a arewa maso gabacin Najeriya, haka zalika 'yan kungiyar sun sace wasu manoman goma sha biyar tare da jikkata wasu da dama a gonakinsu.

Maharan sun yi wa gonakin manoman kawanya ya yin da suke kwashe amfanin gonarsu, wani mazaunin yankin mai suna Ibrahim Liman da ya shaida lamarin, ya ce a 'yan kwanakin nan maharan na Boko Haram da mayakan ISWAP na kara zafafa kai hare-haren ta'addanci a yankunan nasu.

Tuni dai aka kai wadanda suka jikkata a wani babban asibitin garin domin yi masu magani.