Harin gurneti a Mombasa na kasar Kenya
June 25, 2012A kasar kenya, wani harin gurneti da aka kai ya haddasa mutuwar mutun daya tare da jikata wasu dama. Jami'an 'yan sandan kasar sun bayyana cewar an harba gurnetin ne a wata mashayar giyaya da ke birnin Mombasa a jiya lahadi da maraice, a lokacin da ake tsaka da kallo wasan neman lashe kofin kwallon kafa na nahiyar Turai ta kafar telebijin.
Wannan harin ya zo ne kawana daya bayan gardagi da Amirka ta yi cewa akwai yiwuwar fiskantar hare-haren ta'addanci a birnin na Mombasa. sai dai hukumomin Kenya sun soki wannan mataki na amirka, suna masu cewa zai iya kashe guywar baki da ke sha'awar zuwa yawon bude ido a kasar.
Kenya dai ta fiskanci hare-hare da dama tun bayan da tura da sojojinta Somaliya domin yakar 'yan kungiyar al-Shabab a watan disemban bara.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala