Harin kunar bakin wake a birnin Jeddah
July 4, 2016Talla
Harin dai ya wakana da daren ranar Lahadi wayewar wannan Litinin, inda dan kunar bakin waken ya ajiye motarsa a gaban wani babban asibiti da ke kallon karamin ofishin jakadancin na Amirka a birnin Jeddah, kuma ya tashi bam din da ke ciki a daidai lokacin da jami'an tsaron biyu suka zo domin bincikensa a cewar wata majiya ta jami'an tsaro. Gidan talbijin din kasar ta Saudiyya ya tabbatar da wannan hari, inda masu bincike ke kokarin tantance gawar wanda ya kai harin.