1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin London: An karfafa matakan tsaro.

Gazali Abdou Tasawa
June 4, 2017

A Birtaniya hukumomin 'yan sanda sun tabbatar da mutuwar ya zuwa yanzu mutane akalla shida a yayin da wasu sama da 48 suka ji rauni a cikin jerin wasu hare-hare da aka kai a daren jiya Asabar a birnin London. 

https://p.dw.com/p/2e6Xm
England Vorfall auf der London Bridge Mehrere Fußgänger angefahren
Hoto: Picture alliance/empics/D. Lipinski/PA Wire

 

Hukumar 'yan sandar birnin na London ta ce da misalin karfe tara da minti takwas na daren jiya ne wasu mutane uku suka kai harin da wata babbar mota inda suka kutsa a guje cikin taron jama'a a saman wata gadar tsakiyar birnin kana suka fito suka ta daba wa mutane wuka kafin daga bisani 'yan sanda su bindige su. 

Hukumar 'yan sandar birnin na London dai ta bayyana harin da cewa na ta'addanci ne. Da ya ke jawabi a gaban manema labarai Mark Rowley mataimakin babban kwamishinan 'yan sandar birnin na London ya ce sun karfafa matakan tsaro a duk fadin birnin.

"Ya ce muna ci gaba da bincike kuma za mu kara baza jami'an 'yan sanda a cikin birnin na London a kwanaki masu zuwa"


Babbar gadar ta birnin na London dai ta kasance a rufe a duk tsawon daren jiya. Wannan dai shi ne hari na uku da birnin na London ya fuskanta a cikin kasa da watanni uku.