Harin Nairobi-sakacin gwamnatin Kenya
October 4, 2013To har yanzu dai harin da kungiyar al-Shabaab ta kai kan cibiyar cinikaiya dake birnin Nairobin Kenya na ci gaba da daukar hankalin jaridun na Jamus. A labarinta mai taken "Fatali da gargadi kai hari" jaridar Berliner Zeitung cewa ta yi gwamnatin Kenya ta samu labarin yiwuwar kai mata harin ta'addanci sannan sai ta ci gaba kamar haka.
"Gwamnatin Kenya na shan suka game da harin ta'addancin da aka kai kan cibiyar cinikaiya ta Westgate dake birnin Nairobi saboda fatali da gargadin da hukumomin tsaro suka yi mata. Jaridun kasar ta Kenya sun rawaito wani bayani daga hukumar leken asirin kasar inda ciki aka nuna yiwuwar kai harin ta'addanci a kan cibiyar kasuwancin ta Westgate ko a kan majami'ar Katholika ta Holy Family dake tsakiyar babban birnin. Tun a farkon wannan shekara aka yada bayanan sannan aka sake maimaita shi a farkon watan Satumba. Jaridar ta ce hatta hukumomin leken asirin Isra'ila sun yi gargadi game da yiwuwar kai hari kan kadarorin Yahudawa a Nairobi. Wani bangare na cibiyar kasuwancin ta Westagate mallakin Isra'ila ne. Jaridar ta kara da cewa an yi bayani dalla-dalla a cikin gargadin na hukumar leken aisirin Kenyar amma gwamnati ba ta dauke shi da muhimmanci ba."
Boren adawa da gwamnatin Kahrtoum
Mummanar zanga-zanga a Sudan inji jaridar Neue Zürcher Zeitung tana mai tsokaci ga boren adawa da janye tallafin man fetir a Sudan sannan sai ta kara da cewa.
"Hukumomin Sudan sun haramta buga jaridar Al-Intibaha mai sukar lamirin gwamnati. Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da ake gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin ta da komadar tattalin arziki da gwamnati ta fara aiwatarwa. Gwamnatin shugaba Omar al-Bashir ta ce babu gudu babu ja da baya game da matakin da ta dauka na janye tallafin man fetir."
Da ta leka kasar Gambiya har wayau jaridar ta Neue Zürcher Zeitung ta yi sharhi ne game da shawarar da gwamnatin Gambiyar ta dauka na janyewa daga kungiyar Commonwealth ta kasashe renon Ingila. Ta ce:
"Ba tare da wani kwakkawaran dalili ba a ranar Laraba shugaba Yaya Jammeh ya ba da sanarwar ficewar kasar Gambiya daga kungiyar ta Commonwealth wadda ya zarge ta da zama dandalin ci gaba da raya manufofin mulkin mallaka. Sai dai masharhanta sun dangantaka wannan matakin da rama wa kura aniyarta bayan kasashen yamma dake ba Gambiyar tallafi sun zargi hukumomin shari'arta da yanke hukunci iri daban daban ga masu goyon bayan auren jinsi daya."
Ci-gaba a matakan rage yunwa a duniya
Matsalar yunwa a duniya ta kara raguwa inji jaridar Franfurter Allgemeine Zeitung sannan sa ta ci gaba kamar haka.
"Rahoton shekara shekara a kan cimaka da kungiyar abinci da aikin gona ta Majalisar Dinkin Duniya FAO ta fitar a wannan Talata ya nuna cewa ana samun ci gaba mai ma'ana a kokarin cimma muradun karni na rage yawan masu fama da karancin abinci a duniya. Wannan ci-gaban bai tsaya a kasashe masu arziki kadai ba, a nahiyar Afirka ma yawan masu fama da karancin abin sakawa bakin salati ya ragu daga kashi 33 zuwa 25 cikin 100 a tsukin shekaru 20 da suka gabata. FAO ta ce kwanciyar hankalin siyasa da habakar tattalin arziki da inganta manufogin zamantakewar al'umma za su taimaka wajen samun karin kudin shiga ga talakawa."
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar