1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin ramuwar gayya ya janyo mutuwar mutane 10 a Kenya

January 10, 2013

Rigingimun dake da nasaba da zabukan da kasar Kenya za ta gudanar na ci gaba da janyo mutuwar jama'a.

https://p.dw.com/p/17H6a
Kenyan police patrol past smoldering houses that had been burned in the village of Nduru, following renewed clashes between farmers and herders in the Tana River delta area of southeastern Kenya, Tuesday, Sept. 11, 2012. An official says armed raiders killed four people in Kenya's southeast despite a dusk-to-dawn curfew to prevent further clashes between the Orma and Pokomo tribes that have left more than 100 people dead. (Foto:AP/dapd)
Hoto: dapd

Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross da kuma jami'an 'yan sanda sun sanar da cewar mutane 10 ne suka mutu a wannan Alhamis, bayan da wasu mutane dauke da makamai suka cinnawa gidaje da dama wuta a yankunan dake kusa da kogin Tana dake kasar Kenya. Daga cikin mamatan akwai kananan yara biyar da kuma mata biyu, harma da wani dan makarantar dake dauke da jakar littattfansa. 

Kungiyar ta Red Cross da rundunar 'yan sandan dai sun bayyana cewar rigingimun na da nasaba ne da zabukan kasar dake tafe. Wannan rikicin dai wani bangare ne na musayar hare-hare a tsakanin kabilun dake gaba da juna bisa mallakar wuraren kiwo da kuma na kamun kifi. Sai dai a wannan Larabar ce 'yan sanda suka ce akwai 'yan siyasa da kuma 'yan kasuwar da ke ruruta wutar fitinar, wadda ta janyo mutuwar kimanin mutane 100 a cikin watan Agusta. 

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita        : Umaru Aliyu