Hariri ya janye takardar murabus dinsa
December 5, 2017Talla
Hariri ya aike da wannan sako ne ga majalisar ministocin kasar lokacin da ya ta yi zamanta na farko tun bayan da ya koma kasar makonni biyun da suka gabata. Majalisar ta dai ta nuna jin dadinta da wannan matakin da Firaministan ya dauka. Hariri dai ya ce ya yanke hukuncin cigaba da aiki a matsayinsa na jagoran gwamnatin kasar ne in har kungiyar nan ta Hezbolla da ke samun goyon bayan Iran za ta dakatar da yin shisshigi a harkokin siyasar yankin musamman ma dai a kasar Siriya da Yemen.